Babu kuɗi a jam’iyyar APC – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Babu kuɗi a jam’iyyar APC – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yace yawaitan kiraye kiraye da ake samu na muradin raba Najeriya ya biyo bayan tabarbarewa da wargajewar jam’iyyun siyasa ne.

Dayake jawabi ga wasu zababbun manema labaru, Kwankwaso yace an karya lagon jam’iyyun Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Bom ya tashi da ƙananan yara yan ƙunar baƙin wake a Adamawa

“Kamar jam’iyyar mu ce, ko kudin tafiyar da ita ma babu, ba’a zaman tattaunawa da shuwagabannin jam’iyya tun da muka hau madafin iko, haka zalika suma jam’iyyar adawa na cikin rudani da yaki ci yaki cinyewa.” Inji Shi.

Babu kuɗi a jam’iyyar APC – Sanata Rabiu Musa Kwakwaso

Sanata Rabiu Musa Kwakwaso

Sai dai Kwankwaso ya saba da ra’ayin gwamna El-Rufai dake cewa a kama matasan nan da suka baiwa inyamurai wa’adin sallama daga Arewa, inda yace kamata yayi a kira su zuwa tattaunawar sulhu, amma fa a sani raba Najeriya ba shine abu mafi a’ala ba.

Dayake bayani akan shugaban kasa Muhammadu Buhari da zabukan 2019, Kwankwaso yace idan Buhari zai yi takara ba matsala bace, don kuwa rashin lafiya na kan kowa.

NAIJ.com ta kawo muku bidiyon kasurgumin mai garkuwa da mutane:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel