Haraji: Wani babban Dan wasan kwallon Duniya zai wuce gidan yari

Haraji: Wani babban Dan wasan kwallon Duniya zai wuce gidan yari

– Dan wasan PSG Di-Maria bai biya wasu kudin haraji ba

– Angel Di-Maria ya tabbatar da bakin sa cewa bai da gaskiya

– Sai dai da wuya Di-Maria ya shiga gidan kurkuku wannan karo

Bayan Cristiano Ronaldo an kara samun wani Dan wasa da laifin haraji. Dan wasan gaba Di-Maria na Kasar Ajentina bai da gaskiya. Ta tabbata da bakin Dan wasan cewa bai biya wasu kudi ba lokacin yana Garin Madrid.

Haraji: Wani babban Dan wasan kwallon Duniya zai wuce gidan yari

Di-Maria bai biya wasu kudin haraji ba a Sifen

An kama tsohon Dan wasan gaban Real Madrid da Manchester United Angel Fabian Di-Maria da laifin rashin biyan kudin haraji a lokacin da yake kasar Sifen kamar yadda mu ke samun labari daga Jaridun Kasar waje.

KU KARANTA: Dubi wani Dan kwallo a wurin aiki Umrah

Haraji: Wani babban Dan wasan kwallon Duniya zai wuce gidan yari

Dan wasa Di Maria sai gidan yari kenan?

Di-Maria ya tabbatar da kan sa cewa akwai wasu kudi har na Dalar Euro Miliyan £1.14 da ya ki biya kamar yadda doka ta tanada. Hakan dai ta sa aka yanke masa daurin shekara daya a gidan maza. ‘Dan wasan ba zai yi zaman yari ba tun da wannan ne karo na farko da aka kama sa da laifi.

Ku na da labari cewa Dan wasa shi ma Cristiano Ronaldo na shirin barin Real Madrid bayan an fara zargin sa da kin biyan haraji. Shi ma tsohon Kocin na sa Jose Mourinho bai sha ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Charley Boy ya shirya zanga-zanga a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel