El-Rufai ya gaza, ba zai iya mulkin jihar Kaduna ba – Shehu Sani

El-Rufai ya gaza, ba zai iya mulkin jihar Kaduna ba – Shehu Sani

- Bakin rijiya ba wurin wasan yara bane, Shehu Sani ya gargadi El-Rufai

- Shehu Sani ya zargi El-Rufai da mayar da gwamnati tamkar da gidansu

Sanatan Kaduna ta tsakiya, sanata Shehu Sani ya shawarci gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai daya jingine maganan takarar shugaban kasa dayake da sha’awar yi a shekarar 2019.

Sanatan yace mai yau ma tayi ballantana gobe, tun da dai gwamnan ya kasa mulkin Kaduna yadda ta kamata, toh lallai ba zai iya mulkan Najeriya ba, inji Sanatan.

KU KARANTA: Barka: An kammala tashar jiragen ruwa na kan tudu dake Kaduna (Hotuna)

Shehu Sani ya bayyana haka ne a ranar Laraba cikin wata sanarwa daya fitar inda ya danganta yawan garkuwa da mutane da ake yi a jihar da sakacin gwamnan, sa’annan ya zargi El-Rufai da rashin adalci a gwamnatinsa.

El-Rufai ya gaza, ba zai iya mulkin jihar Kaduna ba – Shehu Sani

Shehu Sani da baba Buhari

“El-Rufai na ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa, amma har yanzu bai gayyace shi ya kaddamar da ko da bayan gida ba a jihar Kaduna, sa’annan ga matsalar sace sacen mutane, El-Rufai na son ya dinga danganta kansa da Buhari, amma sune munafukan Buhari.

“Don haka nake kira ga El-Rufai daya jingine muradin tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa ko na shugaban kasa. Haka zalika ya takura ma yan jaridu, yana ta kama su yana daurewa, zuwa yanzu ya kama kimanin guda 7

“A yanzu ya mayar da Kaduna tamkar gidansu na gado, ramin kura daga ke sai yayanki, ba tare da samar da kwakkwaran cigaba ba, sai karairayi a kafafen watsa labaru.” Inji Kwamared Shehu Sani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo muku bidiyon kiranyen Sanata Melaye

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel