Yansanda sun kama Uba da ɗa, da hannu cikin kisan jigon APC (Hotuna)

Yansanda sun kama Uba da ɗa, da hannu cikin kisan jigon APC (Hotuna)

- An kama mutane 8 da ake zargi da hannu cikin kisan wani jigon APC

- An kashe jigon na APC ne a ranar Alhamis din data gabata

Rundunar Yansandan jihar Ondo ta bayyana ma manema labaru mutane takwas da take zargi da hannu cikin kisan gillar da aka yi ma wani jigon jam’iyyar APC, Olumide Odimayo.

An bayyana wadanda ake zargin ne a ranar Laraba 21 ga watan Yuni, kwanaki kadan da kashe Olumide, wanda sai da aka fara sace shi a ranar Alhamis data gabata, daga bisani ne yan banga suka gano gawarsa.

KU KARANTA: Gwarzon Soja ya rasa ransa a hannu Boko Haram (Hotuna)

Cikin wadanda aka kama har da wani uba mai suna Bekewei Francis da yaronsa David Seimengha, sauran sun hada da Fikesi Inuesokan, Evan Roman, Gbamila Success, Bodidi Idowu, Saturday Amos da Ijanboh Kehinde.

Yansanda sun kama Uba da ɗa, da hannu cikin kisan jigon APC (Hotuna)

daya daga cikin mutanen

Kwamishin yansandan jihar Ondo Hilda Ibifuro-Harrison tace: “Da misalin karfe 6 na safiyar ranar Alhamis din data gabata ne aka sace Olumide, da samun labarin lamarin, yansanda tare da yan banga suka bazama nemansa, amma sai muka samu gawarsa, tare da kama mutane 8.”

Yansanda sun kama Uba da ɗa, da hannu cikin kisan jigon APC (Hotuna)

Mutanen da aka kama

NAIJ.com ta ruwaito an samu wayoyi guda 10, alburusai da bindiga kirar AK 47 guda daya a hannunsu.

Yansanda sun kama Uba da ɗa, da hannu cikin kisan jigon APC (Hotuna)

Makamai

Dayake bayanin yadda suka gudanar da aikin nasu, David, yace mahaifinsa Bekewei ne ya gayyace shi tare da wasu mutane dasu je su sace Olumide.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Najeriya giwar Afirka, kalla

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas

Gandireba ya kashe mai yin garkuwa da mutane na boge a kotun Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel