Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

– Maganar tsige Dino Melaye daga Majalisa na ta kara karfi

– Sanatan na Jihar Kogi na cikin babban matsala a halin yanzu

– Melaye dai yace Gwamnan Jihar sa da wannan danyen aiki

Dama kuna da labari cewa Dino Melaye na cikin tsaka mai wuya. Mutanen mazabar sa na Yammacin Kogi na shirin yi masa kiranye. Idan hakan ya tabbata Sanatan zai bar Majalisa ba girma ba arziki.

Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

Sanata Melaye zai bar Majalisa ba girma ba arziki?

KU KARANTA: Matakai na tsige Dan Majalisa a Najeriya

Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

Cikin Sanata Dino Melaye ya duri ruwa

Sanata Dino Melaye na Yammacin Jihar Kogi ya tare su bayan da Hukumar zabe ta kasa watau INEC ta karbi takardun shaida na cewa mutanen mazabar na Jihar Kogi sun zabi a maido Sanatan da su ka zaba gida.

Dama kun dai ji cewa mutane 188,588 su ka sa hannu inda su ka nemi a maido Sanata Dino Melaye gida daga Majalisar Dattawa inda yake wakiltar mazabar sa ta Yammacin Kogi. Kawo yanzu an mikawa Shugaban Hukumar zabe na kasa wannan bayani a jiya.

KU KARANTA: An kama wani Dan Majalisa an rufe; ka ji dalili

Dino Melaye: Daga mai bakin tsiya ya koma wanda kujerar sa ke lilo

INEC na shirin koro Sanata Dino Melaye daga Majalisa Dattawa

Rikicin Gwaman Bello na Jihar da Sanata Dino Melaye ya kai inda ya kai. Sanatan ya zargi Gwamnan Jihar da hannu a cikin yunkurin da ‘yan mazabar sa ke yi na yi masa kiranye wanda yanzu maganar tayi nisa. A baya dai an san Sanatan da yawan shiga cikin rikici ko yanzu ya za a kare?

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana shirin kora Sanata Dino daga Majalisa [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel