An fasa kwai: Ya karbi hanci daga Dangote domin ya hana a tunbuke Sarkin Kano

An fasa kwai: Ya karbi hanci daga Dangote domin ya hana a tunbuke Sarkin Kano

– Kakakin Majalisar Jihar Kano na cikin matsala a halin yanzu

– Kabiru Rurum ya karbi Naira Miliyan 100 daga hannun Dangote

– An ba da wannan cin hanci ne domin ka da a cire Sarkin Kano

Mu na jin labari cewa ana shirin tsige kakakin Majalisar Kano. Dan Majalisar ya karbi cin hanci domin a rufe maganar Sarki. ‘Yan Majalisar na Kano dai sun shirye tsige Shugaban na su.

An fasa kwai: Ya karbi hanci daga Dangote domin ya hana a tunbuke Sarkin Kano

Dan Majalisa ya karbi cin hanci domin a rufe maganar Sarki

Ana shirin tsige kakakin Majalisar Jihar Kano bayan da aka fahimci cewa ya karbi cin hanci har na Naira Miliyan 100 daga hannun Attjirin nan Alhaji Aliko Dangote domin a rufe maganar binciken Sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

KU KARANTA: Mu mu ka hada Shugaba Buhari da aiki Inji APC

An fasa kwai: Ya karbi hanci daga Dangote domin ya hana a tunbuke Sarkin Kano

Rurum ya karyata cewa yakarbi Naira Miliyan 100 daga hannun Dangote

Rahotanni na zuwa mana cewa ‘Yan Majalisa kusan 32 ke shirin tsige Kakakin inda su kace ban da wannan maana ma dai akwai wasu laifuffuka da dama kan shugaban na su. Rurum ya rabawa wasu ‘Yan Majalisar kudi kafin ya tafi aikin Umrah domin ya shawo kan su.

Jiya kun ji cewa wasu ‘Yan Majalisar Tarayya ba su ji dadin kalaman Farfesa Yemi Osinbajo ba, bayan ya zargi ‘Yan Majalisa da yin kari a cikin kundin kasafin bana. Wani ‘Dan Majalisar yace hurumin su ne kuma dole a saki wadannan kudi ko ya ji ba daidai ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kasafin bana kamar dai na kowace shekara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel