Matakai 10 da doka ta tanada wajen koro ‘Dan Majalisa gida

Matakai 10 da doka ta tanada wajen koro ‘Dan Majalisa gida

– Yanzu haka maganar koro Dino Melaye daga Majalisa tayi nisa

– Sanatan na iya barin Majalisa ba girma ba arziki

– Muddin Jama’a su ka ce ba su yi dole ka dawo

NAIJ.com ta kawo maku matakan da ake bi wajen yi wa Dan Majalisa kiranye ganin yadda mutanen mazabar Yammacin Kogi ke shirin yi maido Sanatan su Dino Melaye gida.

Matakai 10 da doka ta tanada wajen koro ‘Dan Majalisa gida

Matakai wajen yi wa 'Yan Majalisa kiranye

KU KARANTA: Dubi abin da wani Dan Majalisa yake yi

1. Sama da rabi na mutanen mazabar su bayyanawa Hukumar zabe cewa ba su yi na’am da Dan Majalisar su ba.

2. Sai a shirya sa-hannu a kananan hukumomi na mazabar a kowane filin zabe

3. Hukumar zabe na kasa INEC za ta sanar da ‘Dan Majalisar halin da ake ciki

4. INEC za ta sanar da lokacin da za a tantance sa-hannun Jama’a

5. Hukumar INEC za ta tabbatar cewa masu zabe ne su ka sa-hannu

6. Za a duba domin a tabbatar da cewa an samu fiye da rabin mutanen mazabar sun ce ba su son Dan Majalisar na su

7. Idan ba a samu adadin da ya dace ba za ayi watsi da maganar a nan ko kuma

8. Za a shirya zaben raba-gardama a mazabar domin a maido Sanatan ko ya cigaba da wakilci.

9. Da zarar mafi yawan Jama'a sun yi na’am da zaman sa ko maido sa gida shikenan

10. Sai Shugaban Majalisa ya fatattako sa a sake sabon zabe

Ku same a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko ya dace a ba mai garkuwa da mutane aiki a Gwamnati

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel