Hukumar Ýansanda ta sallami manyan hafsoshin Ýansanda guda 4

Hukumar Ýansanda ta sallami manyan hafsoshin Ýansanda guda 4

- Hukumar kula da Yansanda ta amince da sallamar manyan hafsoshin Yansanda 4

- Hukumar ta sallame su ne saboda kama su da ayyukan rashin da’a

Hukumar kula da lamurran Yansanda ta amince da sallamar wasu manyan hafsoshin Yansanda har su hudu daga bakin aiki saboda kama su da ayyukan rashin da’a, inji rahoton Premium Times.

Yansanda da sallamar ta shafa sun hada da mai mukamin mataimakin kwamishina guda daya, da masu rike da mukamin mataimakan sifritenda su uku.

KU KARANTA: Atiku ya fara shirin fafatawa da Sule Lamido a takarar shugaban ƙasa 2019

Kaakakin rundunar Yansanda ta kasa Ikechukwu Ani ne ya sanar da hakaa ga manema labaru a Abuja a ranar Laraba 21 ga watan Yuni. Inda ya kara da cewa a yanzu haka hukumar ta ja kunnen wasu manan jami’an ta guda takwas.

Hukumar Ýansanda ta sallami manyan hafsoshin Ýansanda guda 4

Ýansanda guda 4

Ani yace hukumar ta amince da mayar da ofisoshin ta guda 14 bakin aiki bayan sauraron korafe korafen su, tare da yin watsi da koke koken wasu tsofaffin yansanda da aka sallama a baya su 11.

Daga karshe Ani yace tuni aka aika ma Sufeto janar da hukunce hukunce don bayar da umarnin aiwatar dasu, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Attajirin mai garkuwa da mutane

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel