Jama’an mazabar Sanata Dino Melaye sun miƙa takardun yi masa kiranye ga hukumar zaɓe

Jama’an mazabar Sanata Dino Melaye sun miƙa takardun yi masa kiranye ga hukumar zaɓe

- Al'ummar mazabar Kogi ta yamma sun shirya yi ma sanatansu kiranye

- Jama'an sun aika ma hukumar zabe, INEC takardun korafe korafen su

Jama’an daga mazabar Kogi ta yammda wadanda Sanata Dino Melaye ke wakilta sun mika takardar koke ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, inda suke bukatar yi masa kiranye.

NAIJ.com ta ruwaito shugaban al’ummar mazabar, Cif Cornelius Olowo yana bayyana ma kamfanin dillancin labaru, NAN, a sakatriyar INEC dake Abuja cewa jama’an mazabar Dino sun yanke shawarar dawo dashi gida.

KU KARANTA: Gwarzon Soja ya rasa ransa a hannu Boko Haram (Hotuna)

Olowo yace sun samu sa hannun sama da kashi 52 na jama’an mazabar, ya kara da cewa jama’an sun yanke shawarar yi masa kiranyen ne sakamakon rashin tabuka komai a mazabar.

Jama’an mazabar Sanata Dino Melaye sun miƙa takardun yi masa kiranye ga hukumar zaɓe

Sanata Dino Melaye

“A shekaru biyu da suka wuce, sanatoci da dama suna komawa mazabarsu suna jin ra’ayoyin al’ummarsu, amma banda sanata Melaye, sau daya ya tattauna da mu jama’ansa, gaba daya ya yanke kafa daga wajen mu.

“A yanzu muna da sama da masu katin zabe 360,000 a mazabar mu, kuma zuwa yanzu mun samu sa hannun sama da mutane 188,500 masu sha’awar yi ma sanatan kiranye. Saura INEC ya rage tayi aikinta kawai.” Inji Olowo

Jama’an mazabar Sanata Dino Melaye sun miƙa takardun yi masa kiranye ga hukumar zaɓe

Yayin da ake mika takardun ga INEC

Shima Daraktan wayar da kan masu zabe na hukumar INEC, Oluwole Osace-Uzzi ya tabbatar da karbar takardun muradin kiranyen Sanata Melaye, inda yace a ranar Laraba 21 ga watan Yuni aka suka karba.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda aka shirya yi ma Melaye kiranye:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel