Bom ya tashi da ƙananan yara yan ƙunar baƙin wake a Adamawa

Bom ya tashi da ƙananan yara yan ƙunar baƙin wake a Adamawa

- Wasu mata yan kunar bakin wake su biyu sun yi kacakaca da kawunansu

- Lamarin ya faru ne lokacin da suka yi kokarin kai hari a Adamawa

Wasu mata yan kunar bakin wake su biyu sun yi kacakaca da kawunansu sa’ilin da suka kai wani hari a kauyen Tsamiya, dake karamar hukumar Madagali, inji rahoton Daily Trust.

Yan kauyen sun bayyana cewar yan matan sun samu shiga kauyen a asirce, amma basu samu nasarar cimma gaci ba, kafin wasu mafarauta suka gane su, suka dakatar dasu.

KU KARANTA: Danjuma da Danjumai: ‘Yan Darika da ‘Yan Shi’a ‘Yan uwa ne Inji Shehun Tijjaniyya

Sakataren kungiyar mafarautan Najeriya, Garba Tarfa ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace “Mafarauta ne suka gano yan matan a kauyen tsamiya, amma koda suka nemi dasu yi saranda, sai daya daga cikinsu ta tada bom dinta, duka su biyu suka mutu.”

Tarfa ya danganta yawan hare haren da ake samu a kauyukan da rashin ko karancin dakarun Soji a yankunan, inda ya roki hukumomi dasu turo jami’an tsaro da isassun kayan aiki.

“Babu Sojoji a yankin nan na Madagali, wannan shine ke baiwa yan ta’addan daman kawo hare hare, a satin data gabata ma sun kai hari kauyen Wagga, inda muka samu nasarar kama mutum 3 a cikinsu, muka kais u Yola.” Inji shi.

Sai dai hukumomin Soji sun musanta samun labarin kai harin, Kaakakin bataliya ta 28 dake Mubi Major Barde Akintoye yace basu da masaniya akan harin, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Attajirin mai garkuwa da mutane

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel