Tattalin arziki: Dala ta gagara tashi sama a hannun 'Yan kasuwa

Tattalin arziki: Dala ta gagara tashi sama a hannun 'Yan kasuwa

– Babban bankin Najeriya ya dage wajen ganin Dala ta yi kasa

– CBN ya saki sama da Dala Biliyan 5 a kasuwa

– Yanzu dai Dalar ba ta wuce N364 a hannun ‘Yan kasuwa

Tsarin CBN na sakin Dala dai yayi aiki ba shakka. Yanzu haka Dalar ta makale ne a kan N364. Abubuwa dai sun fara gyaruwa cikin ‘yan kwanakin nan.

Tattalin arziki: Dala ta gagara tashi sama a hannun 'Yan kasuwa

Darajar Naira na karuwa a halin yanzu

Ba shakka tsarin Babban bankin Najeriya na CBN na sakin Daloli yayi aiki yayin da Dala ta makale a kan N364 kawo yanzu haka da muke magana. Idan ba a manta ba dai an saida Dalar a kan sama da N520 a kwanakin baya.

KU KARANTA: Kudin makamai: An damke tsohon hafsun Soji

Tattalin arziki: Dala ta gagara tashi sama a hannun 'Yan kasuwa

Darajar Naira na karuwa a halin yanzu

Gwamnan Babban bankin CBN ya saki akalla Dala Miliyan 195 a wannan makon cikin kasuwa domin cigaba da sauko da farashin Dala. Kafin nan dai Dalar na kan N367 wanda yanzu haka an samu raguwar N3 kenan.

Wani babban Jami’in CBN ke cewa tattalin arzikin Najeriya zai zabura zuwa karshen shekarar nan. Sanannen abu ne dai cewa Najeriya na cikin matsin tattali kusan tun bayan hawan Shugaba Buhari wanda yanzu abubuwa sun kama hanyar mikewa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Anya kudin Najeriya zai taba kamo Dalar Amurka?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel