Babu maganar tursasawa Jama’a addinin Musulunci a Najeriya

Babu maganar tursasawa Jama’a addinin Musulunci a Najeriya

– Gwamnatin Tarayya ta kauda duk wani zargi game da maganar wasu Fastoci

– Wasu na ganin akwai makarkashiya na tursasawa ‘Yan Najeriya Musulunci

– Gwamnatin kasar dai ta yi watsi da wannan maganar kamar yadda za ku ji

Wasu na ikirarin cewa an soke ilmin addinin Kirista daga darussan Sakandare. Haka kuma ana yada cewa an saka larabci da ilmin addinin musulunci. Ma’aikatar ilmi dai ta wanke duk wannan zargi dalla-dalla.

Babu maganar tursasawa Jama’a addinin Musulunci a Najeriya

Akwai maganar tursasawa mutane musulunci a kasa?

Gwamnatin Tarayya ta musanya zargin da ke yawo na cewa an soke ilmin addinin Kirista daga darussan makaruntun Sakandare. Gaskiyar maganar dai ita ce tun lokacin tsohon Shugaba Jonathan aka fara wani garambawul a tsarin ilmin kasar.

KU KARANTA: Biyafara: Shehin Malamin addini ya ba Gwamnati shawara

Babu maganar tursasawa Jama’a addinin Musulunci a Najeriya

Gwamnatin Buhari na kokarin murkushe mu Inji Fasto Solomon

Yanzu haka dai an maida darusan addinin musulunci da na kiristanci wuri guda inda kowane dalibi zai dauki wanda ya dace karkashin wani darasi na dabam. Haka kuma an kawo yaren Larabci tare da na Faransanci ga duk mai bukata amma babu dole a lamarin.

Fitaccen Faston nan Johnson Solomon yace Gwamnatin Buhari na kokarin murkushe addinin Kiristanci a kasar nan. Faston yace an soke ilmin addinin Kirista daga darasin makarantu kuma aka bar na Arabi da Musulunci. Wannan magana dai ba daidai ba ce sam.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kudin Najeriya dai ya wargaje. Dubi abin da Jama'a ke fada a Bidiyo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel