Majalisar dattawa na shirin wata kaidin cire Ibrahim Magu daga ofis

Majalisar dattawa na shirin wata kaidin cire Ibrahim Magu daga ofis

- Har yanzu Sanatoci basu wuce fushinsu game rashin cire Ibrahim Magu da fadar shugaban kasa tayi duk da cewan ta ki tabbatar da shi

- Yan majalisan na shirin wata kaidin fadawa barayin gwamnati cewa suyi watsi da duk gayyatar da hukumar EFCC tayi musu

- Amma wata majiya tace suna shirya wannan kaidi ne domin hana wasu yan majalisa masu kasha a gindi amsa gayyatar hukumar

An bada rahoto cewa Majalisar dattawan Najeriya na shirya wata kaidi wanda zai wajabta ma fadar shugaban kasa cire shugaban hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu.

Har yanzu Sanatoci basu wuce fushinsu game rashin cire Ibrahim Magu da fadar shugaban kasa tayi duk da cewan ta ki tabbatar da shi.

Wata majiyar cikin gida ta bayyanawa jaridar Vanguard a daren jiya Talata cewa sanatocin na fusace bisa kunnan kasha da fadar shugaban kasa keyi.

Majalisar dattawa na shirin wata kaidin cire Ibrahim Magu daga ofis

Majalisar dattawa na shirin wata kaidin cire Ibrahim Magu daga ofis

Majiyar wacce aka sakaye sunanta tace yan majalisan na shirin nunawa fadar shugaban kasa cewa bata isa ta raina musu hankli ban a rashin daukan shawaransu na cire Ibrahim Magu.

Majiyar tace yan majalisan na shirin fadawa yan Najeriya cewa kada su sake amsa gayyatar hukumar EFCC a duk lokacin da tayi kira.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta turke Kenneth Minimah

Amma wata majiya tace suna shirya wannan kaidi ne domin hana wasu yan majalisa masu kasha a gindi amsa gayyatar hukumar

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel