Safarar makamai: Hukumar EFCC ta turke tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Kenneth Minimah

Safarar makamai: Hukumar EFCC ta turke tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Kenneth Minimah

- Har ila yau hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tana binciken kudin safarar makamai

- Tsohon shugaban hafsan sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Kenneth Minimah ya sha tambayoyi a ofishin EFCC

- EFCC tace yawancin cinikayyan sayan makaman da akayi ba bisa ga doka ba ne

Wata rahoton jaridar The Nation ta nuna cewa tsohon shugaban hafsan sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Kenneth Minimah ya kwashe sa’o’ I yau Talata yana amsa tambayoyi a ofishin hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.

Game da cewan rahoton, ana bincikan Minimah ne saboda wani zargin almundahanan da akayi wajen sayen makaman biliyoyin kudi.

Safarar makamai: Hukumar EFCC ta turke tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Kenneth Minimah

Safarar makamai: Hukumar EFCC ta turke tsohon shugaban hafsan sojin kasa, Kenneth Minimah

Tsohon shugaban hafsan sojin kasan Najeriya, Laftanan Janar Kenneth Minimah ya rike kujeran ne tsakanin 16 ga Janairu 2014 zuwa 13 ga Yuli 2015.

Hukumar EFCC na binciken sama da kudi $1,891,809,299.1 da akayi amfani da su wajen sayan makamai.

KU KARANTA: An garkama wani dan majalisar tarayya

Banda Minimah, akwai sauran hafsoshi 53 da za’a bincika game da wannan almundahanan da akayi.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel