Zaben 2019: Jam'iyyun 15 sun kafa sabuwar jam'iyyar da zai fafata da APC, PDP da APGA a 2019

Zaben 2019: Jam'iyyun 15 sun kafa sabuwar jam'iyyar da zai fafata da APC, PDP da APGA a 2019

- Wasu jam’iyyu siyasa 15 sun kafa jam’iyya mai suna Mega Coalition wanda zai fafata da jam’iyyun APC, PDP da kuma APGA

- Jam’iyyun kawance sun amince da cewar zasu fitar da ‘yan takarar gwamnoni da na shugaban kasa guda daya

- Jam’iyyun kawance sun zabi Cif Perry Opara ya jagorance su

Hadin gwiwar jam'iyyun siyasa 15 sun kafa wata babban jam’iyya wanda aka sani da Mega Coalition, jam’iyyar ta sha damaran fitar da 'yan takara a zaben gwamnaoni da kuma na shugaban kasa a Najeriya.

Jam'iyyun kawancen sun tabbatar wa majiyar NAIJ.com cewar kowane jam’iyyar na damar fito da dan takarar a zaben kansiloli, shugabanin kananan hukumomi, majalisar dokokin, majalisar wakilai da kuma sanatoci, amma za a hada hannu don fitar da dan takara gwamna da kuma na shugaban kasa.

Wasu daga cikin jam'iyyun da suka sanya hannu kan yarjejeniyar daftarin aiki sun hada da jam’iyyar Allied Congress Party of Nigeria ACPN, Better Nigeria Progressive Party BNPP, Democratic Alternative DA, Democratic Peoples Congress DPC da kuma Democratic Party Peoples DPP da sauransu.

Zaben 2019: Jam'iyyun 15 sun kafa sabuwar jam'iyyar da zai fafata da APC, PDP da APGA a 2019

Jam'iyyun kawance sun ce zasu fafata da APC, PDP da APGA a 2019

KU KARANTA: Zaben 2019: ‘Yan siyasan Kudu sun fitar da sunaye 6

NAIJ.com ta ruwaito cewa jam’iyyun kawance sun zabi Cif Perry Opara ya jagorance su kuma zai din ka amsa sunan "Chancellor" a matsayin shugaban jam’iyyun kawance.

Chancellor, Cif Opara, wanda kuma shi ne shugaban jam’iyyar Unity Party na kasa ya yi Allah wadai da kalaman rabuwar kasar da wasu ke furtawa a kwanan nan, ya bukaci 'yan siyasa da kuma mambobin kungiyoyi wadda ba na gwamnati ba, da kuma kungiyoyin zamantakewa da al'adu su yi hankali da wasu kalamai da suke furtawa domin a iya cimma zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani jami'in jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel