'Mu muka jika wa Buhari aiki' inji John Oyegun, shugaban jam'iyyar APC

'Mu muka jika wa Buhari aiki' inji John Oyegun, shugaban jam'iyyar APC

- Buhari yana iya kokarin sa wajen magence matsalolin da ya gada daga gwamnatin baya

- Muna alfahari da nasarorin da muka samu a bangaren noma

- Muna fata Shugaba Buhari ya samu lafiya domin ya cigaba da aikin da ya fara.

Shugaban jami'iyar APC na kasa John Oyegun ya ce Shuga Buhari yana fuskantar kalubale masu dumbin amma duk da haka baiyi kasa a gwiwa ba wajen magance su.

A wata sanarwa da ta fito daga bakin mataimakin hulda da jama'a na APC Edegbe Odemwingie yace a ranar laraba lokacin da ya tarbi wata tawagar yan jami'iyar a karkashin jagorancin Jibril Adamu da Abdullahi Maje a Abuja, Oyegun ya fada wa tawagar cewa jami'iyar tana aiki ba kama hannun yaro domin kara hadin kan yan jami'iyar sakamakon merja da sukayi.

KU KARANTA KUMA: Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

'Mu muka jika wa Buhari aiki' inji John Oyegun, shugaban jam'iyyar APC

'Mu muka jika wa Buhari aiki' inji John Oyegun, shugaban jam'iyyar APC

Ya cigaba da cewa harkan gina kasa aiki ne mai wahala amma shugaba Buhari ya sami nasarori a 'bangarori daban daban.

"Aikin da shuga Buhari ya gada abu ne mai mattukar wahala domin gwamnatin baya bata tabuka komai ba face almubazarranci da dukiyar al'umma, rashin biyan albashi da sauran hakkuna na mai aikata da karfafa cin hanci da rashawa. Wannan ya jefa kasar a matsanancin hali kuma har illa yau ga faduwar darajar man petur a kasuwanin duniya.

"Wannan shi ya haifar da matsanancin halin da mutane ke fuskanta a yanzu. Ina fata da addua Shugaba Buhari ya samu lafiya domin ya dawo ya cigaba da ayyukan da ya fara. Shuga Buhari yana kokarin samar da wasu hanyoyin kudin shiga domin kasa ta rage dogaro akan man fetur.

"Babu wata siddabaru da zamu iya yi domin gyara yana daukan lokaci. Ina alfahari da nassarorin da muka samu a fanin noma musaman shinkafa a jihohin Kebbi, Zamfara, Jigawa da dai sauransu. Mutane suna amfani da shinkafar da muke noma wa a gida kuma da izinin Allah muna fata mu fara fitar da ita wasu kasashen duniya domin samun kudin shiga."

Shugaba Buhari dai ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo domin yaje jinya.

Ku biyo mu a shafukan mu na sada zumunta,

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel