Bikin Sallah: Gwamnan jihar Bauchi ya biya albashin watan shidda

Bikin Sallah: Gwamnan jihar Bauchi ya biya albashin watan shidda

- Gwamnatin jihar Bauchi ta biya ma'aikata kudin albashin wannan wata tun ranar 20 ga wata

- Ta yi hakan ne saboda ma'aikatan suyi shagalin sallah karama cikin walwala da jin dadi

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed A Abubakar ya biya ma'aikatan jihar albashin su na wannan watan da muke ciki a ranar 20 ga watan Yuni, saboda ma'aikatan su yi bukukuwan Sallah cikin walwala.

Idan dai ba a mance ba, haka Mai Girma Gwamnan yayi a watan da ya gabata inda ya biya ma'aikatan tun ranar 26 ga wata (kafin fara azumin watan Ramadan).

KU KARANTA KUMA: Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

Bikin Sallah: Gwamnan jihar Bauchi ya biya albashin watan shidda

Bikin Sallah: Gwamnan jihar Bauchi ya biya albashin watan shidda

Gwamnan Bauchi dai ya kasance daya daga cikin gwamnoni kalilan a fadin Najeriya da suka biya duk albashin Jahar (harda wanda ya samu ana bin Jahar kafin hawansa karagar mulki na tsawon wata uku).

A halin yanzu dai ma'aikatan basa bin bashin albashi ko na wata guda, haka zalika 'yan fansho.

Sanarwar ta fito ne daga Shamsudeen Lukman Abubakar, Mataimaki na musamman ga Gwamnan na jihar Bauchi a fannin sadarwa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel