Wani tsohon minista ya karyata yin sheka zuwa APC

Wani tsohon minista ya karyata yin sheka zuwa APC

- Tsohon ministan ma'aikatar tsaro, Sanata Musiliu Obanikoro ya ƙaryata zargin cewa ya sauya sheka zuwa APC

- Obanikoro ya ce ya halarci taron sanata Remi Tinubu domin ayyuka alherin da take yi a mazabar Legas ta tsakiya

- Obanikoro ya ci gaba da cewa yanzu haka ya dawo gida don ya ci gaba da zama da mutanensa

Tsohon ministan ma'aikatar tsaro, sanata Musiliu Obanikoro a ranar Talata, 20 watan Yuni ya muzanta labarin da yake yawo a kafofin yada labarai cewa ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa PDP zuwa jam'iyyar APC.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar jigon dan siyasan ya bayyana hakan ne a wata taron kai bishara wanda sanata Remi Tinubu, uwargidan shugaban jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta shirya a mazabar ta da ke Legas.

Sanata Obanikoro, wanda ya wakilci mazabar jihar Legas ta tsakiya daga shekara 2003 zuwa 2007 wanda ita kuma sanata Remi Tinubu ta ke wakilta yanzu, ya ce: " Na so wannan wurin ne yau domin na bayyana maku cewa ina tare da ku, kuma nazo don in zauna ne, Allah ya albarkace ku. Na gode". Inji Obanikoro.

Obanikoro ya karyata yin sheka zuwa APC

Musiliu Obanikoro da shugaban kasar Kodebuwa, Alassane Quattara

Halartar wannan taron da kuma kalamansa ya janyo jita-jitar da ke yawo a kafofin watsa labarai cewa tshon sanatan ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Obanikoro dai na hannun daman Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne wanda shine gwamnan jihar Legas a wancan lokacin, 2005 ne tsohon ministan ya sauya sheka daga jam’iyyar Alliance for Democracy wato AD zuwa jam’iyyar PDP inda ya yi kokarin zama gwamnan jihar Legas a shekara ta 2007.

KU KARANTA: Kotu ta kama wani Dan Majalisa bayan ya kasa kawo mai laifi

Duk da haka, tun lokacin da ya dawo Najeriya bayan da ya yi hijira zuwa kasar Amurika bayan da gwamnatin jam’iyyar PDP karkasshin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ta sha kayi a zabbukan da ta gabata, Obanikoro ya nizanci kansa daga PDP kuma ya sulhunta da Tinubu.

Bayan halartar taron sanata Tinubu, Obanikoro ya ƙaryata zargin cewa ya sauya sheka zuwa APC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dattawan arewa sun ki amince da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya zama shugaban kasa a 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel