Karda a ba ‘yan Igbo kasar Biyafara – Dahiru Bauchi ga gwamnatin tarayya

Karda a ba ‘yan Igbo kasar Biyafara – Dahiru Bauchi ga gwamnatin tarayya

- Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da karda ta yarda ta ba ‘yan kabilar Igbo kasar Biyafara

- Ya ce a maimakon haka a da su da sauran kabilu a tattauna don kawo ci gaban kasar

- Daga karshe ya bukaci matasan Arewa da su janye barazanar da sukayi na korar yan Igbo daga yankin

Babban malamin nan na musulunci kuma shugaban kungiyar Tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da karda ta yarda ta ba ‘yan kabilar Igbo kasar Biyafara a maimakon haka ta zaunar da su da sauran kabilu a fadin kasar don tattaunawa kan yadda za’a kawo ci gaban tattalin arziki da kuma zaman lafiya mai dorewa a Najeriya.

Da yake jawabi ga manema labarai a Kano, a jiya, Sheikh Dahiru Bauchi ya ce karfin dake tattare da kasar Najeriya shi ya bata damar kasancewa a saman sauran kanana kasashen Afrika, tare da yawan mutanen ra wanda hakan yasa kasar ta zamo aljanna ga masu zuba hannun jari sannan kuma ta kasance abokiyar dukkan kasashen duniya ta fannin tattalin arziki.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Magu na neman wata tsohuwar Ministar Jonathan

Karda a ba ‘yan Igbo kasar Biyafara – Dahiru Bauchi ga gwamnatin tarayya

Karda a ba ‘yan Igbo kasar Biyafara inji Dahiru Bauchi ga gwamnatin tarayya

A cewar sa wadanda ke fafutukar neman Biyafara ba’a ma haife sub a lokacin da akayi yakin basasa sannan kuma cikin su babu wanda zai iya fadin ribar da za’a samu idan aka kuma yakin basasa a kasar dake dauke da mutane sama da miliyan 150.

Ya yi bayanin cewa ci gaban Najeriya zai yiwu ne idan dukkan bangarorin zasu zauna a karkashin inuwa daya sannan kowa yay i abunda al’adarsa da addininsa ya yarda da shi.

Sheikh Bauchi ya yi kira ga matasan yankin Arewa da su janye takobin su kan wa’adin da suka ba ‘yan Igbo na barin yankin.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel