Wa’adin Igbo : Abinda Osinbajo ya tattauna da sarakunan Arewa a Aso Rock

Wa’adin Igbo : Abinda Osinbajo ya tattauna da sarakunan Arewa a Aso Rock

A jiya Talata, 20 ga watan Yuni, mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya gana da sarakunan gargajiyan Arewa akan wa’adin da wasu matasan Arewa suka baiwa yan kabilar Igbo.

Zaku tuna cewa ya kamata ayi ganawar ranan Litinin ne amma aka daga.

A ganawar, Osinbajo ya sanar da shirin gwamnatin tarayya na kare mutuncin Najeriya a matsayin kasa guda daya. Ya fahimci cewa shugabannin gargajiya na da rawan takawa a harkokin gudanar da kasa.

Yace: “ Mu a matsayin gwamnati, zamu tabbatar da cewa mun yi amfani da duka abinda gwamnati ke da shi wajen tabbatar da cewa babu wanda yayi barazanar ga kasancewar kasa guda wanda ya kunshi rayuwan dan Najeriya a kowani sashen kasa.

Wa’adin Igbo : Abinda Osinbajo ya tattauna da sarakunan Arewa a Aso Rock

Wa’adin Igbo : Abinda Osinbajo ya tattauna da sarakunan Arewa a Aso Rock

“Manufarmu shine samar da kasa wacce zata cigaba, kasa wacce mutane zasu iya neman halaliyarsu cikin kwanciyar hankali ba tare da banbancen-banbancen addini ko kabila ba,”.

KU KARANTA: Wani dan majalisa yayi barazanar tsige Osinbajo

Wannan shine karo na biyu da shugaba Osinbajo zai gana da masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya a cikin wannan mako.

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel