Kotu ta kama wani Dan Majalisa bayan ya kasa kawo mai laifi

Kotu ta kama wani Dan Majalisa bayan ya kasa kawo mai laifi

– An garkame wani Dan Majalisar a karshen makon jiya

– Dan Majalisar ya gagara kawo wani da ake tuhuma

– Honarabul Aliyu Pategi na wakiltar mazabar Edu a Majalisa

A Ranar Juma’a aka rufe wani Dan Majalisar Tarayya. Dan Majalisar ya gaza kawo wanda ya tsayawa da ake tuhuma. Yanzu dai Allah yayi an sake shi bayan ya sha zaman kaso.

Kotu ta kama wani Dan Majalisa bayan ya kasa kawo mai laifi

Babban Kotun Tarayya a Najeriya

Kuna da labarin cewa an garkame wani Dan Majalisar Tarayya a karshen makon jiya bayan da wanda ya tsayawa a Kotu tayi dabo yayin da ake shirin zaman shari’a. Bayan da Alkali ya neme ta ya rasa aka bada umarni a rufe Dan Majalisar na Jihar Kwara.

KU KARANTA: Shugaban Majalisa Bukola Saraki yana Umrah

Kotu ta kama wani Dan Majalisa bayan ya kasa kawo mai laifi

Wani Dan Majalisar Tarayya yayi zaman kaso

Yanzu dai an gano wannan mata da ake tuhuma Madam Akinjide wanda hakan ta sa aka saki Hobarabul Aliyu Pategi mai wakiltar mazabar Moro da Edu da Pategi na Jihar Kwara a Majalisar Wakilan Tarayya.

Hukumar EFCC mai yaki da zamba ta gayyaci wata tsohuwar Ministar harkokin jirgin saman Najeriya Stella Oduah bisa wasu zargi. Yanzu haka dai Madam Stella Oduah Sanata ce a Majalisar Dattawa inda ta ke wakiltar Arewacin Jihar Anambra.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An yi wani zanga-zanga a Legas [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel