Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

- Wannan shine tarago na karshe na ganawa da jama'a da shugaba Osinbajo keyi

- Ana neman mafita kan batun ballewar Najeriya

- Osinbajo na son zaunar da Najeriya yadda aka bar masa ajiyarta

A kokarin sa na ganin bata ruguje a hannunsa ba, mukaddashin shugaba Buhari na ta kokarin ganin ya rike amanar da aka damka masa ta kasa guda daya Najeriya, inda yake ta zaman tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tafiyar da jama'a, ciki harda sarakuna da gwamnoni, daga bangarorin kasar nan.

A taragon karshe na wannan zama dai, a yau shugaban yana zama da gwamnoni jihohi 36 domin duba yadda za'a shawo kan matsalolin tsaro da ma na hana tashin tashina a kasa.

A baya ma dai, NAIJ.com ta ruwaito muku irin wannan tattaunawa da shugaban yayi da sarakunan gargajiya da na addinai da ma na siyasa daga bangarorin kasar nan.

Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

Osinbajo zai gana da gwamnoni 36 kan batun Bayafara

Wannan duk ya biyo bayan kokarin farfado da kasar Biyafara wadda aka dakile ta garin kabilun Ibo, wanda ya jefa Najeriya yakin basasa a shekarun baya. An kuma sami wasu samari su kuma daga arewa, da ke baiwa kabilun kudu mazauna arewa wa'adin su fice su bar kasar arewar.

A yanzu dai, an fi ada karfi kan batun hadin kan kasa, da ma kuma sake tsara Najeriyar yadda kowa zai more arzikin yankinsa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni ne ke bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC
NAIJ.com
Mailfire view pixel