Sabbin hare-haren kabilanci a jihar Taraba, duk da dokar takaita yawo

Sabbin hare-haren kabilanci a jihar Taraba, duk da dokar takaita yawo

- Har yanzu fadace-fadace basu kare ba tsakanin kabilun Kasarnan

- A jihar Taraba ana da banbance banbance sosai na kailu da addinai

- An sake samun barkewar rikici duk da cewa ana kan kafiw

A cikin yanayin kafiw na takaita fitar rana da dare, an sake samun barkewar rikici a jihar Taraba yankin Sardauna, bayan wanda aka samu a baya. garuruwa da kauyuka da dama ne dai aka sake farma a daren jiya, inda aka sami asarar rayuka, shanu da ma kone gidaje da dukiyoyi.

Wasu tsageru da ake kira mambila milisha ne dai ake zargi da harin, wanda rahotanni ke cewa sun kai harin kan Mayo Ndaga.

Jama'ar yankin dai da suka tagayyara sun kira gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo musu dauki, domin asarar da suka yi.

Sabbin hare-haren kabilanci a jihar Taraba, duk da dokar takaita yawo

Sabbin hare-haren kabilanci a jihar Taraba, duk da dokar takaita yawo

"Muna shan ruwan azumi suka far mana, kuma da kyar muka sha, duk da cewa sun kone mana gari sun kuma kada shanunmu sun yi awon gaba da su.," inji Malam Musa Hassan mazaunin Mayo Ndaga, wani yanki na fulani.

Ya zuwa yanzu dai ba'a ji daga bakin gwamanti ko hukumar yansanda na yankin ba.

A baya-bayan nan dai, ana samun karuwar tashin hankula a jihar ta Taraba, mai nasaba da kabilanci da ma addinanci.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel