Majalisar Dattijai na duba yiwuwar hana mutane kin amsa gayyatar EFCC

Majalisar Dattijai na duba yiwuwar hana mutane kin amsa gayyatar EFCC

Ana ganin hakan baya rasa nasaba da son da majalisar ke yi na takura bangaren zartaswa na su tsige shugaban EFCC din bayan kin tantance shi don tabbatar dashi kan kujerar sa, wadda a yanzu rikon kwarya yake shekaru biyu.

Majalisar Dattijai na duba yiwuwar zaka dokar kin bin umarni ko ziyarta ko girmama gayyatar da duk za'ayi ma wani da sunan bincike daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, domin wai cewa shugaban haramtacce ne tunda basu tabbatar dashi ba, har karo biyu.

Kin tabbatar da Magu dai, bisa zargin cewa shima yana da kashi a wando, bayan rahoton sirri da hukumar 'yansandan ciki ta DSS ta fitar a kansa, na nufin sai dai shugaba Buhari ya sauke shi ya turo wani, wanda kin yin hakan a wurinsu, na nufin raini ne wai.

Majalisar Dattijai na duba yiwuwar hana mutane kin amsa gayyatar EFCC

Majalisar Dattijai na duba yiwuwar hana mutane kin amsa gayyatar EFCC

Shi dai wanda ya bayar da wannan labari ya so a boye sunansa, amma a cewarsa, majalisar ta dukufa wajen ganin ta wargaje zaman shugaban a kujerarsa.

A gefe daya kuma, zargin cin hanci da wankiya da kin bayar da asalin yawan dukiyarsa ga hukuma, wadda ake yi wa shugaban majalisar dattijan, Sanata Bukola Saraki, na iya zama yana da nasaba da wannan ramuwa ganin cewa an kori karar daga kotun CCT, an kuma wanke Dattijon, bayan shari'ar shekaru biyu.

A makon nan dai gwamnatin tarayya ta hannun EFCC din ta daukaka kara, domin dai a samu abin da za'a sauke shi shugaban majalisar, wanda ya hada kai da jam'iyyar PDP don zama shugaban Majalisar, tare da goyon bayan wasu na jam'iyyarsa ta APC.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel