Mayakan Boko Haram sun kaiwa motoci 200 ciki harda na 'yan sanda Hari

Mayakan Boko Haram sun kaiwa motoci 200 ciki harda na 'yan sanda Hari

- Mayakan Boko Haram sunyi wa jami'ai kwanto

- Ayarin motocin da suka farma sun kai 200

- Ance sunyi sha fatattaka amma an rasa mutum biyu

A rahotanni da ke fitowa daga dajin sambisa, muna samun labarun cewa mayakan Boko Haram sunyi kwanton bauna sun kai hari kan wani babban ayarin gwamnati dake wucewa ta garin Damboa, a hanya da aka kwato kuma aka bude daga mayakan na Boko Haram.

A rahoton dai mayakan Boko haram ne, dauke da muggan makamai suka farma ayarin motoci 200 da suke hanyar su ta zuwa aiki bayan kwaso 'yan sanda daga kudancin kasar nan, inda aka far ma ayarin da harbe harbe, an kuma sami asarar rayuka ciki harda dansanda daya da ma wani direban gwamnati, an kuma ce sunyi awon gaba da matan 'yan sanda da ke ayarin.

Mayakan Boko Haram sun kaiwa motoci 200 na 'yansanda Hari, sun kuma sace mata

Mayakan Boko Haram sun kaiwa motoci 200 na 'yansanda Hari, sun kuma sace mata

Mista Damian Chukwu, kwamishinan yan sanda na Maidugurin, ya tabbatar da harin inda yace an sami asarar rayuka biyu. A cewarsa tun da aka bude hanyoyin, motoci suna samun 'yan rakiya 'yansanda, saboda a da sojoji kadai ke iya bin yankin.

A cewar wadanda harin ya rutsa dasu, sunce a daidai Dalwa ne abin ya abku, kuma maharan sun kai harin ne ta hanyar lababo wa ta bayansu, bayan motocin tsaro sun wuce gaba.

A yanzu dai an ci karfin mayakan Boko Haram, amma kuma suna da karfin iya kai hare hare a kan yankunan da ke kewaye da dajin Sambisa, wanda hakan ya saka aka kasa mayar da masu gudun hijira daga yankin komawa gida.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC
NAIJ.com
Mailfire view pixel