Bayan yayi nasara a Kotu: Dubi inda aka ga Sanata Bukola Saraki

Bayan yayi nasara a Kotu: Dubi inda aka ga Sanata Bukola Saraki

– Shugaban Majalisar Dattawa ya leka kasa mai tsarki

– Kwanan nan Bukola Saraki yayi nasara a Kotu

– Majalisa dai ta tafi hutu yayin da ake shirin kammala azumi

Yayin da Majalisa ke kira a rage kudin aikin hajji. Bukola Saraki ya leka kasar Saudiyya domin Umrah. Ba a dade da Kotu ta wanke Saraki daga zargin da ke kan sa ba.

Bayan yayi nasara a Kotu: Dubi inda aka ga Sanata Bukola Saraki

Dubi Shugaban Majalisar Dattawa a kasa mai tsarki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya leka Kasa mai-tsarki Saudiya domin ibadar Umrah kamar yadda NAIJ.com ta samu labari a jiya. Dama dai Majalisa ta tafi hutun Sallah yayin da ake shirin kare azumi.

KU KARANTA: Kasafin kudi: Majalisa na shirin tsige Osinbajo

Kuna sane cewa kwanan nan Bukola Saraki yayi nasara a Kotu bayan an dade ana zargin sa da laifi wajen bayyana kadarorin sa wanda tuni Gwamnati ta daukaka karar. Musulmai da dama dai na aikin Umrah cikin watan na Ramadan.

A baya wani Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Sokoto Sanata Ibrahim Abdullahi da wasu Sanatocin kusan 40 sun nemi Hukumar kula da aikin Hajji na kasa watau NAHCON ta rage kudin kujerar aikin Hajji na wannan shekarar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kasafin kudin bana tamkar na bara

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel