Rochas: 'Bama bukatar Bayafara'

Rochas: 'Bama bukatar Bayafara'

- Gwamna Rochas ya ce kabilar ibo na bukatar Najeriya

- Samarin kabilar Ibo na son kafa kasar Bayafara

- An shekara hamsin da hambare kasar Bayafara

A ci gaba da ake na cece-kuce tsakanin kabilu daga bangarorin kasar nan, Gwamnan jihar Imo ta kudancin Najeriya, wadda ke cikin yankunan da ke iya zama karkashin kasar Bayafaran, yace su kam a jihar sa basu bukatar Bayafara, ya kuma ce kabilar Ibo gaba-daya basu bukatar wannan sabuwar kasa.

A lalube da ake na kokarin shawo kan kabilanci da bangaranci da ya addabi samarin kasar nan, gwamnatin Tarayya na ta zaman shawarwari da jami'an tsaro, da ma sarakunan gargajiya don gudun kar a sami matsalar tsaro tsakanin kabilun Najeriya.

Gwamna Rochas, ya tsawatarwa da masu son kafa kasar da zimmar balle wa daga kasar nan, kan cewa kada su so tada fitina, kamata yayi su kara karfin dangantaka tsakanin kabilun guda biyu.

Rochas: 'Bama bukatar Bayafara'

Rochas: 'Bama bukatar Bayafara'

Hadimin yada labarai na jihar Sam Onwuomeodo ne ya bada sanarwar da sa hannun gwamnan inda ya ce kamata yayi kabilu su zauna su yi sulhu da juna.

"Duk da cewa samarin arewar nan dai suna da laifi, domin yadda suka zuzuta abin, muma namu samarin suna da laifin tunzuri, dole a kula ayi hankali kar abin ya zamo rikici," inji sanarwar.

Ana dai yi wa Rochas Okorocha na jam'iyyar APC kallon mai iya hado kan kabilar Ibo domin zabuka masu zuwa, musamman idan yana cikin tikitin zama shugaba ko mataimakin kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel