'Akwai makarkashiya kan kasa kama samarin Arewa' - Sarkin Delta

'Akwai makarkashiya kan kasa kama samarin Arewa' - Sarkin Delta

- Ana zargin Malam Nasir El-Rufai na Kaduna da kasa kama samarin arewa

- Sarkin Edo yace Najeriya tayi espaya

- Yayi kira da a sake tsara Najeriya

A masarautar Siemberi a jihar Delta, Sarki Charles Ayeni-Botu, ya yi kira da a sake tsara Najeriya bisa tsarin gaskiya, inda kowanne bangare zai ci gashin kansa da arzikinsa, dalili da cewa kasar da Lord Lugard ya kafa a 1914, tati espaya a 2014.

Sarkin ya kuma zargi gwamnatin tarayya da ta jihar Kaduna kan kasa kama samarin arewa da suka ce sai kabilar Ibo sun bar yankin. Inda ya ce wannan na nuna makarkashiya da goyon baya kan samarin da gwamnati da dattijan yankin ke basu.

"Kana so ka ce min yanzu a sati biyun nan da suka wuce, samarin sun gagari hukumar 'yan-sanda ne? shugaban 'yansanda IGP da gwamna Nasir El-Rufai sun bada sammacin kame samarin nan, amma shiru kake ji, sai ma kara karfafa kiran nasu suke yi," cewar sa.

'Akwai makarkashiya kan kasa kama samarin Arewa' - Sarkin Delta

'Akwai makarkashiya kan kasa kama samarin Arewa' - Sarkin Delta

Sarki Charles na Siemberi dai shine tsohon shugaban yankunan kasar nan masu arzikin man fetur.

"Lokaci yayi da za'a sake tsara Najeriya, tun da dai kowa ya gaji da juna, sai a koma tsarin gaskiya. Duba da dama dai tsarin da Lord Luggard ya dora mu a kai ya shekara 100.

"Gashi dai ana da rahoton tattaunawar kasa da aka yi tun 2014, wato Nationa Conference, amma an kasa aiwatar dashi, wanda hakan ne kadai zai hana tarwatsewar kasar baki daya, dole ne a guji kashe kashen kabilanci na 1966-67," Ya kara da cewa.

Ana dai kokarin shawo kan lamarin na son a rarrabe kasar nan tsakanin kabilun yankuna daban daban, a matakai daban-daban.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa

Hukumar NDLEA ta kama kwayoyi kilogaram 1000 a Jigawa
NAIJ.com
Mailfire view pixel