Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo ya dauki wani babban mataki

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo ya dauki wani babban mataki

– Mukaddashin Shugaban kasa ya dauki wani mataki a Gwamnati

– Farfesa Osinbajo ya amince da sauyin wasu Sakatarorin Gwamnatin

– Ofishin Shugaban Ma’aikata na kasa ya tabbatar da wannan

Farfesa Osinbajo ya sauyawa wasu Ma’aikata wuraren aiki. Mohammed Bukar na Ofishin Sakataren Gwamnati na cikin wanda aka taba. Haka kuma an sauyawa Roy Ugo da Abubakar Magaji ofis.

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo ya dauki wani babban mataki

Osinbajo ya sauyawa Sakatarorin Din-din-dini wuri aiki

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya amince da wasu sauye-sauye da aka yi wa wasu Sakatarorin Din-din-din na Gwamnatin Tarayya guda biyu kamar yadda Ofishin Shugaban Ma’aikata ya fitar.

KU KARANTA: Majalisa na barazanar tsige Osinbajo

Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo ya dauki wani babban mataki

Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo

An maida Injiniya Abubakar G. Magaji daga ma’aikatar ayyuka zuwa ma’aikatar harkokin cikin gida. An kuma cire Mohammed Bukar da Dr. Roy Ugo daga Ofishin Sakataren Gwamnati zuwa ma’aikatar ayyuka.

Jiya mun ji cewa wata Kungiyar hadakar Arewa ta nemi Mukaddashin Shugaban kasar Najeriya Farfesa Osinbajo ya kyale Inyamurai su bar kasar zuwa duk inda za su je. Shugabannin Kungiyar sun ce ba matsala don an ba Kasar Ibo ‘Yancin su.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Har yanzu na da martaba a Afrika [Bidiyon ra'ayin Jama'a]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel