Kasafin kudi: Idan Osinbajo yayi mana wata-wata sai mu tsige sa - Inji Dan Majalisar Tarayya

Kasafin kudi: Idan Osinbajo yayi mana wata-wata sai mu tsige sa - Inji Dan Majalisar Tarayya

– Wani Dan Majalisar Tarayya ya soki Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo

– Dan Majalisar yace idan Farfesa Osinbajo yayi wata-wata sai su tsige sa

– Farfesa Osinbajo ya zargi ‘Yan Majalisa da yin cushse a cikin kasafin bana

Wasu ‘Yan Majalisa ba su ji dadin kalaman Farfesa Yemi Osinbajo ba. Farfesan ya zargi ‘Yan Majalisa da yin kari a cikin kundin kasafin bana. Wani ‘Dan Majalisar yace hurumin su ne kuma dole a saki wadannan kudi ko su yi yunkurin tsige sa.

Kasafin kudi: Idan Osinbajo yayi mana wata-wata sai mu tsige sa - Inji Dan Majalisar Tarayya

Majalisa na shirin tsige mukaddashin shugaban kasa?

Abu Sadiqu ya rahoto cewa wasu ‘Yan Majalisar Tarayya sun soki Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo bayan ya zargi ‘Yan Majalisar kasar da yin kari a cikin kundin kasafin bana. ‘Dan Majalisar yace doka ta ba su damar hakan kuma idan bai yarda ba ya tafi Kotu.

KU KARANTA: Majalisa ta yaudari Osinbajo Inji Dan Majalisa

Kasafin kudi: Idan Osinbajo yayi mana wata-wata sai mu tsige sa - Inji Dan Majalisar Tarayya

Wani Dan Majalisa yayi barazanar tsige Osinbajo

Wani Dan Majalisar yake cewa duk ayyukan da aka kara na cigaban kasar ne kuma dole fadar shugaban kasar ta saki wadannan kudi idan ba haka ba, Majalisa ba za ta amince da wata magana nan gaba ba.

Kwanaki Farfesa Yemi Osinbajo ya sa hannu kan kasafin kudin bana. Osinbajo yace ba a samu aringizo daga sashen zartarwa ba sai dai illa an samu wasu sauye-sauye ne daga Majalisa wanda ya ja aka kara bata lokaci.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko ya dace a ba Evans aiki a Gwamnati?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya

Ana muzgunawa Matan Musulman da ke karatun shari’a a Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel