Kungiyoyin matasan arewa sun karyata zargin cewar suna wasan buya da Jami'an tsaro a Kaduna

Kungiyoyin matasan arewa sun karyata zargin cewar suna wasan buya da Jami'an tsaro a Kaduna

- Babu kamshin gaskiya a labarin da ake yadawa na cewar shuwagabannin kungiyoyin matasan arewa na wasan buya da jami'an tsaro a kaduna

- Shuwagabanin sun jaddada matsayin su cewar nan da ranar 1 ga watan Oktoba dole ne ‘yan kabilar Igbo su fice daga arewacin kasar

- Matasan sun ce a kungiyance sun sha alwashin daukar matakai na shari'a ga dukkanin wata kafar yada labarai da tayi musu karya

Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya 16 sun fito fili sun nesanta kansu da wani labari dake yawo a wasu kafafen yada labarai cewa, matasan sun fara wasan buya da jami'an tsaro tun bayan umarnin da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufa'I ya bayar na cewa a kama su a duk inda aka gan su.

Da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna, Alhaji Nastura Ashiru Sherrif daya daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan, ya ce wannan labari da wata jarida ta turanci ta buga karya ce tsagwaronta kuma wata manakisa ce ake son a kulla domin jefawa jama'ar arewa shakku a kansu, inda yace babu wani abu makamancin haka da ya faru, babu wata kafar yada labarai da suka zanta da ita a kan wannan magana, sannan kamfanin jaridar da ya buga wannan labari na kanzon kurege tuni ya nemi gafararsu a kan haka, kuma su a kungiyance sun sha alwashin daukar matakai na shari'a ga dukkanin wata kafar yada labarai da tayi musu karya.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin Rariya, Ashiru Sheriff ya kara da cewar zaman lafiyar Najeriya ne ya sanya suka bukaci kabilar Igbo da su gaggauta barin yankin arewa cikin watanni 3, domin su Igbo sune suka fito fili suka bayyana cewar ba sa bukatar zama a Najeriya ba, zai dai a raba kasa su koma yankin su, sannan suka yi barazanar cewa matukar ba a saurari bukatar su ba to za suyi dukkannin mai yiyuwa wajen haddasa yaki a Najeriya domin sun mallaki muggan makamai, Inji su. Wannan shine dalilin da yasa kafin akai ga haka mu matasan arewa muka bukaci da su koma kasar tasu cikin ruwan sanyi.

Kungiyoyin matasan arewa sun karyata zargin cewar suna wasan buya da Jami'an tsaro a Kaduna

Alhaji Nastura Ashiru Sherrif daya daga cikin shugabannin kungiyoyin matasan arewa

KU KARANTA: El-Rufa'i ya sha alwashin hukunta matasan Arewa

Kungiyar matasan na arewa sun kara da cewar suna nan akan bakarsu na korar Inyamurai daga arewa kafin nan da ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, kuma jama'a su sani wannan mataki da suka dauka sunyi ne domin kishin arewa da kuma zaman lafiyar kasa baki daya, domin haka babu wata maganar buya da suke yi, suna walwalarsu ko ina a cikin arewacin kasar, kuma dukkanin wasu masu hankoron kama su ai sun san su, kuma sun san inda suke, saboda haka babu gudu ba ja da baya Inyamurai dole su bar arewa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ku saurari bayanai mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a kan yakin basasa ta Biafra

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel