Kamar Messi, Neymar da Ronaldo, Jose Mourinho na fuskantar tuhumar zamba a Spain

Hukumomi a kasar Spain suna tuhumar kocin kulob din Manchester United, Jose Mourinho, bisa zambar haraji a lokacin da yake kocin kulob din Real Madrid.

Masu shigar da kara na tuhumar kocin da zambatar kasar Spain euro miliyan 3.3 (wato kimanin dala miliyan 3.6) na kudin haraji tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012.

NAIJ.com ta samu labarin cewa kawo yanzu Mourinho bai ce uffan ba tukuna.

Kamar Messi, Neymar da Ronaldo, Jose Mourinho na fuskantar tuhumar zamba a Spain

Kamar Messi, Neymar da Ronaldo, Jose Mourinho na fuskantar tuhumar zamba a Spain

A kwanakin baya ne hukumomin kasar Spain suka tuhumi wasu manyan 'yan wasan kwallon kafa da zambar haraji.

Ciki har da dan wasan Barcelona Lionel Messi, wanda a halin yanzu ke fuskantar zaman kaso na watanni 21 da kuma Cristiano Ronaldo na Madrid da sauransu.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Naji dadin yafiyar da akayi wa Rahma Sadau - Rabi'u Rikadawa

NAIJ.com
Mailfire view pixel