Kotu a Kano ta kawo wa Gwamna Ganduje mummunan cikas

Kotu a Kano ta kawo wa Gwamna Ganduje mummunan cikas

Babbar kotun jihar Kano ta dakatar da gwamnatin jahar daga karban kudin haraji. Sabuwar tsarin karbar kudin harajin da gwamnatin jihar ta fito da shi na amsan haraji ga masu ababen hawa samfurin kurkura da ‘yan Adai-daita Sahu ya ci karo da cikas, bayan da babbar kotun Jihar ta yanke hukuncin dakatar da gwamnantin Kano daga karbar harajin.

Gwamnatin Kano na karbar harajin N100 ne a hannun masu ababen hawa kama daga Adaidaita Sahu zuwa Kurkura da makamantansu harajin N100 a kulliyaumin, inda kuma Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba daya karkashin mai rikon babban Jojin Jiha Justice Nura Sagir Umar ta zartas da hukuncin haramtawa hukumar tattara haraji karbar kudin harajin masu ababen hawa a nan Kano.

Kotu a Kano ta kawo wa Gwamna Ganduje mummunan cikas

Kotu a Kano ta kawo wa Gwamna Ganduje mummunan cikas

NAIJ.com ta samu labarin cewa mai Shari’a Nura Sagir Umar ya yanke hukuncin dakatar da duk wani Jami’in hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ko jami’in KAROTA ko ma wani mai damara tare masu Kurkura ko Adaidaita sahu ko makamancinsu da nufin karbar haraji, har sai kotun ta kammala sauraron karar da aka shigar gabanta.

Wasu mutane ne dai suka shigar da gwamnatin Kano da kwamishinan Shari’a da wasu mutane 29 kara bisa zargin saba ka’idar yarjejeniyar da aka kulla tun farko.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel