YANZU YANZU: An samu sassan mutane a gidan wani tsoho mai shekaru 80

YANZU YANZU: An samu sassan mutane a gidan wani tsoho mai shekaru 80

- Tsohon kauyen Gbogan wanda ke karkashin karamar hukumar Ayedade a jahar Osun na cikin wani sabon tashin hankalin a yayin da aka samu rubabbun sassan jikin mutane a cikin wani gida a garin.

- Rubabbun kawunan mutane 3 tare da wasu sassan jikin mutane daban daban an gan su ne a cikin wani gida ai dakuna 4 a Idifa ta filin Ile-Eesu da ke Gbogan.

An samu gano rubabbun sassan mutanen ne sanadiyyar macifar wari da ta addabi jama’a da ke yankin, wadanda suka janyo hankalin mutane mazauna yankin zuwa ga gida wanda hakan kuma ya sa aka gudunar da bincike a kan gidan.

NAIJ.com ta samu labarin cewa a lokacin da wasu matasa suka shiga gidan wanda gidan wani mutumi ne mai shekara 80 a duniya, mai suna Lamidi Abioye wanda hi ke zama a cikin gidan shi kadai yayin da ya baza sassan mutane a ko ina cikin gidan.

YANZU YANZU: An samu sassan mutane a gidan wani tsoho mai shekaru 80

YANZU YANZU: An samu sassan mutane a gidan wani tsoho mai shekaru 80

A yanzu haka an mika shi tsohon hannun ‘yan sanda sannan kuma rubabbun sassan mutane da aka samu a gida na wurin su a matsayin shaida.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda reshen jahar Osun, SP Folasade Odoro ya ce wanda ake zargi bayyana cewa shi mai maganin gargajiya ne. Odoro ya tabbatar da cewa za’a gudunar da bincike na musamman game da al-amarin sannan kuma shi kuma wanda ake zargi za a shigar da karan shi don a ma shi shari’a kamar yadda doka ta tsara.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel