Bankunan Najeriya za su kwace iko daga Etisalat ta Najeriya

Bankunan Najeriya za su kwace iko daga Etisalat ta Najeriya

- Akwai zammani wasu bankunan Najeriya za su kwace kamfanin sadarwa ta Etisalat

- Gamayyar wasu bankunan Najeriya na bin Etisalat bashin kimanin naira biliyan 541.8

- Rukunin kamfanin Etisalat da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, ya janye hannun jarinsa daga Etisalat ta Najeriya

Gamayyar wasu bankunan Najeriya ta ce zata kwace ikon kamfanin Etisalat saboda ya gaza biyan bashin da suke bin sa.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da rukunin kamfanin Etisalat da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, ya janye hannun jarinsa kashi 70 cikin 100 daga Etisalat ta Najeriya.

Kamfanin sadarwa na Emerging Markets Telecommunication Services Limited, wanda ke rike da sauran kashi 30 na hannun jarin a Etisalat, ya gaza biyan bashin da bankunan ke bin sa.

Bankunan Najeriya za su kwace iko daga Etisalat ta Najeriya

Gamayyar wasu bankunan Najeriya na bin Etisalat bashin kimanin naira biliyan 541.8

Gamayyar bankunan, wadda bankin Access ke jagoranta, na bin Etisalat bashin dallar Amurka biliyan 1.72 (kimanin naira biliyan 541.8) wanda kamfanin ya ranta a shekara 2015.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, batun kwace ikon Etisalat din dai ya janyo fargaba ga ma'aikatan kamfanin.

KU KARANTA: Hukumar Kastam ta kwace shinkafa mai kimanin kudi N14 Million

Sai dai a wata sanarwa da hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa, NCC, ta yi da manema labarai, ta tabbatarwa masu mu'amala da Etisalat cewa su daina fargaba.

Sanarwar, wacce kakakin hukumar NCC Tony Ojobo ya sanya wa hannu, ta ce "hukumarmu tana tabbatarwa masu layin Etisalat 21m cewa zata yi dukkan abin da ya dace bisa doka domin ganin sun ci gaba da more amfanin da layukan waya na Etisalat".

Mista Ojobo ya kara da cewa NCC tana daukar matakai masu muhimmanci wurin ganin ba a kwace iko da bankunan za su yi da Etisalat bai yi mummunan tasiri ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

'Yan Najeriya na tambaya ko naira 1 na Najeriya zai iya sake zama dallar Amurka 1 a kasuwan canji?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel