Kasafin kudin bana: Majalisa ta yaudari Osinbanjo – Abdulmuminu Jibrin

Kasafin kudin bana: Majalisa ta yaudari Osinbanjo – Abdulmuminu Jibrin

- Abdulmumin Jibrin ya ce mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi kasada da ya sanya hannu a kasafin kudin 2017

- Ya ce Osinbanjo ya yi la’akari ne kawai da alkawarin da majalisar ta yi na yin sauye-sauye

Dakataccen dan majalisar wakilai Abdulmumin Jibrin ya bayyana sanya hannu a kasafin kudin bana da mukaddasshin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbanjo ya yi a matsayin kasada.

A wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, Jibrin ya ce ga dukkan alamu majalisar wakilan a wannan karan ta yaudari mukaddashin shugaban kasar.

Ya ce wannan shine karo na farko tun shekarar 1999 da wani shugaba ya sanya hannu a kasafin kudi saboda kawai alkawarin da majalisa ta yi na cewar za ta aiwatar da gyare-gyaren da bangaren zartarwa ya gabatar.

KU KARANTA KUMA: El-Rufa'i ya sha alwashin hukunta matasan Arewa

Jibrin ya bada misalin da shekarar 2016, yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki zanya hannu a kasafin kudin duk da matsa lamba da barazanar ya dinga samu daga wajen majalisar. Ya ce Buhari sai da ya tabbatar an kammala duk wani gyare gyare kafin ya sanya hannu a kasafin.

Ya ce a bangaren mukaddashin shugaban kasa Osinbanjo kuwa, ya yi la’akari ne kawai da alkawarin da majalisar ta yi na yin sauye-sauye.

Jibrin ya ci gaba da cewa, babu shugaban kasar da ya taba yadda ya yi irin wannan kasada ta kasafin kudi, saboda zai kasance ne kamar shiga yarjejeniya da mutum mara alkawari.

Ya ce ko dai wannan lamari zai haifar da da mai ido ko aa, za a gani a nan gaba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel