El-Rufa'i ya sha alwashin hukunta matasan Arewa

El-Rufa'i ya sha alwashin hukunta matasan Arewa

- El-Rufai ya sha alwashin ganin an hukunta shugabannin kungiyoyin matasan Arewa da sukayi ma kabilar Igbo barazana

- Ya kuma bukaci shugabannin Igbo da su ja kunnuwan matasansu

- Yan Igbo mazauna Arewa sun ce babu inda zasu duk da barazanar kungiyoyin matasan na Arewa

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i ya sha alwashin ganin an kamo tare da hukunta shugabannin kungiyoyin matasan Arewan nan da suka yi barazana ta hanyar ba 'yan kabilar Igbo wa'adin watanni uku na ficewa daga yankin Arewacin kasar.

KU KARANTA KUMA: Sai dai ku mutu: Ronaldo ba zai bar kulob din sa ba Inji Kungiyar Real Madrid

El-Rufa'i ya sha alwashin hukunta matasan Arewa

El-Rufa'i ya sha alwashin hukunta matasan Arewa

Har ila yau gwamnan ya bukaci shugabannin kabilar Igbo wadanda suka kai masa ziyara da cewa dole ne su ma su ja kunnuwan matasan su kan su daina furta kalaman da ke barazana ga ci gaban Najeriya a matsayin tsintsiya madaurin ki daya.

A nasu bangaren, Shugabanannin 'yan kabilar Igbo mazauna Arewa sun yi ikirarin cewa ba za su taba barin yankin ba duk da wa'adin da matasan Arewan suka ba su inda suka yaba wa gwamnatin tarayya kan irin matakan da ta daukasakamakon wannan barazanar.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya

Shehu Sani ya gargadi sabon shugaban Laberiya
NAIJ.com
Mailfire view pixel