Daruruwan masu karban haraji da gwamnatin Kano ta dauka aiki sun ajiye aikinsu

Daruruwan masu karban haraji da gwamnatin Kano ta dauka aiki sun ajiye aikinsu

- Wasu daga cikin masu karban haraji da gwamnatin Kano ta dauka aiki kwanakin baya sun ajiye aikinsu

- Hukumar tara haraji ta jihar (KIRS) ta dauki jami'ai 765 da nufin cimma kudurin hukumar na tara kudaden haraji watanni 3 da suka gabata

- Jami’an sun ajiye aikin sakamakon abunda suka kira rashin cika masu alkawurran da gwamnati ta daukar masu

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewa daruruwa daga cikin ma'aikatan hukumar tara haraji da gwamnatin jihar ta dauka aiki kwanakin baya sun ajiye aiki saboda karancin albashi.

Kimanin watanni 3 kenan gwamnatin Kano ta gudanar da taron yaye jami'ai 765 da ta dauka aiki a hukumar tara haraji ta jihar (KIRS) da nufin cimma kudurin hukumar na tara kudaden haraji akalla naira biliyan 10 duk karshen wata daga 2018.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin Hausa Times, ta ruwaito cewa yanzu kimanin mutum 300 daga cikinsu suka ajiye aikin sakamakon abunda suka kira rashin cika masu alkawurran da aka daukar masu ba a cikin yarjejeniyar aikin.

KU KARANTA: Kano: Za a Fara biyan malamai firamare a jihar Kano

Ana biyan jami'an albashin naira 35,000 sabanin yadda sukayi tunani ganin cewa ance za'a rika biyansu albashi ninkin abunda suke karba a wuraren ayyukansu da suka baro.

Bayanai sun nuna galibin ma'aikatan sun kammala karatunsu na jami'a a yayinda wasunsu kuma ke matakin aiki (albashi) na 8, wasu kuma na 9 wasu kuma suna mataki na 10.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhaus

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile faruwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma

Yadda Gwamnan jihar Kebbi da jami'an tsaro suka dakile afkuwar wani rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma
NAIJ.com
Mailfire view pixel