An kori wasu yan sanda 2 da suka karbi cin hancin 15,000

An kori wasu yan sanda 2 da suka karbi cin hancin 15,000

- An sallami wasu jami’an ‘yan sanda biyu daga aikinsu sakamakon karbi cin hanci

- Jami’an biyu sun karbi 15,000 a hannu wani dan acaba, inda shi kuma ya korafinsa ga rundunar ‘yan sandan

- ‘Yan sandan sun zargi dan acaban da da laifin karya dokar futular bada hannu ta titi

Rundunar yan sandan Najeriya ta kori wasu jami'anta 2 masu aikin bada hannu wato trafic warden sakamakon kamasu da karbar cin hancin naira 15,000 daga hannun wani dan acaba a birnin Abuja.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 29 ga watan Maris da ta gabata. A inda dan acabar ya garzaya sashin kai korafi na rundunar ‘yan sandan ya gabatar da kokensa.

A cewar mutumin yan sandan sun caje shi da laifin karya dokar futular bada hannu ta titi a inda suka takura masa har saida suka tafi dashi banki ya ciro 15,000 ya basu a matsayin kudin sasantawa.

An kori wasu yan sanda 2 da suka karbi cin hancin 15,000

Musa Muktari da Shuaibu Suleman dukan su a ofishin ‘yan sanda na Wuse a Abuja

KU KARANTA: Hukumar yan sanda ta cafke gungun matasa yan fashin da dan shekara 22 ke jagoranta (Hotuna)

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Sufeto janar na yansandan Najeriya, Ibrahim Idris ya ce bayan da hukumar ta gano lamarin ta kori Musa Muktari, mai lamba; 394120 GDI da Shuaibu Suleman, mai lamba; 10627 GDII, dake aiki a ofishin ‘yan sanda na Wuse a Abuja.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu

Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a birnin Shehu
NAIJ.com
Mailfire view pixel