Yaro mai shekaru 16 ya yi wa ‘Yar shekaru 14 fyade a Katsina

Yaro mai shekaru 16 ya yi wa ‘Yar shekaru 14 fyade a Katsina

- An kama wani yaro mai shekaru 14 a duniya kan zargin yiwa yarinya yar shekaru 14 fyade har juna biyu ya shiga

- Wannan mummunan al'amari ya afku ne a wani kauye dake jihar Katsina

An zargi wani matashi mai shekaru 16 a duniya da aka ambata da suna Abdulmalik Yau da laifin yi wa yarinya ‘yar shekaru 14 a duniya mai suna Amina fyade, wanda har ya kaita ga samu juna biyu.

Mummunan al'amarin ya afku ne a kauyen Durbi ta Kusheyi dake karamar hukumar Mani a jihar Katsina.

Rahotanni sun kawo cewa Abdulmalik da Amina dai suna zaune ne a gida daya, amma ba a bayyana dangantakar dake a tsakaninsu ba.

KU KARANTA KUMA: Dubun wasu ɓarayi ta cika, Anyi musu ɗaurin demon minti (Hotuna)

Mahaifin Amina, Murtala Lawal shi ya kai kara wajen ‘yan sanda, inda su kuma suka mika yaron ga kotu.

Mai shari’a Hajiya Dikko ta umarci a tsare yaron a kurkukun yara kafin ranar 20 ga watan Yuli yayin da za a ci gaba da sauraran karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yi shirin ma wani sanata kiranye:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara

An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara

An fara: INEC ta kaɗa gangan siyasar 2019, ta sanya ranakun gudanar da zaɓen fidda yan takara
NAIJ.com
Mailfire view pixel