Dalilin da yasa Najeriya ba zata warware ba – Inji Osinbajo

Dalilin da yasa Najeriya ba zata warware ba – Inji Osinbajo

- Mukaddashin shugaban kasa ya bayyana cewa ba zai goyi bayan wani yunkurin raba kasar nan ba

- Osinbajo yace ya gana da kungiyoyi daga arewa da kuma kudu maso gabashin sassa na kasar kuma sun amince dole Najeriya ta ci gaba da zama tsinsiya mazaunin daya

- Fadar gwamnatin tarayya ta shirya cin abincin dare na iftar da sarakunan gargajiya daga arewacin kasar

Mukaddashin shugaban kasa , Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana dalilin da yasa ba zai goyi bayan wata kungiyar masu fafutukar ficewa daga Najeriya ba.

Osinabjo ya ce bayan jerin ganawa da kungiyoyi daga arewa da kuma kudu maso gabashin sassa na kasar, inda duk mahalartar taron sun amince da cewa dole kasar Najeriya ta ci gaba da zama tsinsiya mazaunin daya.

NAIJ.com ta ruwaito cewa, kakakin mukaddashin shugaban kasa, Laolu Akande ya bayyana hakan a cin abincin dare na iftar wanda shirya a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni a fadar shugaban kasa da sarakunan gargajiya na arewacin kasar.

Dalilin da yasa Najeriya ba zata warware ba – Inji Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa , Farfesa Yemi Osinbajo na gaisawa da sarakunan gargajiya daga arewacin kasar

KU KARANTA: Osinbajo ya yanke shawarar dage zamansa da sarakunan Arewa

A cewar Osinbajo: “Yadda abubuwa ke faruwa a kasar nan yanzu ba muda zabi ila mu zauna a matsayin daya.”

Osinbajo ya ce: “A ganawar da na yi da sarakunan gargajiya daga kudu maso gabashin kasar sun amince da cewa dole ne Najeriya ta zama daya. Idan aka yi la’akari da yawan jinin da aka zubar a kan hadin kai na kasar da kuma kasar nan ta zama daya.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Cikakken bayanin mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo kan yakin basasan Najeriya a cikin wannan bidiyon

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna, kalli hotunan su

NAIJ.com
Mailfire view pixel