Bikin Sallah: Yan fansho sun nemi wata muhimmiyar bukata daga Osinbajo (KARANTA)

Bikin Sallah: Yan fansho sun nemi wata muhimmiyar bukata daga Osinbajo (KARANTA)

- Yan Fansho sun koka akan kudin Fansho a bikin Sallah

- Kungiyar ta nemi Mukaddashin shugaban kasa ya biya su

Kungiyar yan fansho ta roki mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo daya taimaka ya biya su kudin sun a fansho kafin Sallah, inji rahoton Daily Trust.

Kungiyar ta yan fansho ta fitar da sanarwar ne a garin Abuja a ranar Talata 20 ga watan Yuni ta bakin Babban sakataren ta, Actor Zal, inda yace rashin biyan hakkokinsu ka iya shigar dasu matsanancin hali, musamman a lokacin bukukuwan Sallah.

KU KARANTA: Yadda aka kai ma Musulmai masallata hari a birnin Landan (Bidiyo)

Actor ya bayyana cewar yan fansho sun dogara ne kacokal da kudin fansho, sa’annan ya yaba ma Osinbajo da yadda ya saki kudin fanshon nasu na watan data gabata, don haka ya sake yin wannan aikin alheri.

Bikin Sallah: Yan fansho sun nemi wata muhimmiyar bukata daga Osinbajo (KARANTA)

Yemi Osinbajo

Sakataren ya roki Osinbajo daya taimaka ya matsa ma gwamnoni dasu tabbata sun biya albashi da fansho kafin Sallah, kamar yadda ya shaida ma majiyar NAIJ.com.

Bugu da kari, kungiyar tace yayanta sun karkashe yan kudaden su akan hidimar azumin watan Ramadana, don haka babu wasu kudi da suka rage na bikin Sallah.

“Muna yi ma mukaddashin shugaban kasa kyakkyawan zato domin mun san yana sauraron bukatarmu, don haka muke rokonsa daya taimaka mana ya biya mu hakkokin mu ko mayi shagulgulan Sallah cikin annashuwa.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wani mutum ya musulunta:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasa Sanchez zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel