Sai dai ku mutu: Ronaldo ba zai bar kulob din sa ba Inji Kungiyar Real Madrid

Sai dai ku mutu: Ronaldo ba zai bar kulob din sa ba Inji Kungiyar Real Madrid

– Dan wasan Real Madrid Ronaldo ba zai tashi daga Kungiyar ba

– Kungiyar ta bayyana wannan kamar yadda mu ka samu labari

– Shugaban Kungiyar yace babu wanda su ke da niyyar saidawa

Cristiano Ronaldo ba zai bar Kungiyar Real Madrid ba. Haka kuma dai babu ‘Dan wasan da zai tashi. Shugaban Kungiyar Perez ya bayyana wannan ba kwanan nan.

Sai dai ku mutu: Ronaldo ba zai bar kulob din sa ba Inji Kungiyar Real Madrid

Babu in da Ronaldo zai je Inji Real Madrid

Florentino Perez wanda shi ne Shugaban Kungiyar Real Madrid ya bayyana cewa ba za su saida babban Dan wasan su Cristiano Ronaldo ba a wannan shekarar. Akwai kishin-kishin din cewa Dan wasan na shirin barin Real Madrid.

KU KARANTA: Ka ji abin da zai sa Ronaldo ya bar Real Madrid

Sai dai ku mutu: Ronaldo ba zai bar kulob din sa ba Inji Kungiyar Real Madrid

Ba za mu saida kowa ba – Inji Shugaban Real Madrid

Perez ya tabbatar da cewa babu ‘Dan wasan da su ke da niyyar saidawa wanda asali ma dai babu wanda ya nemi daya daga cikin ‘Yan wasan sa. Duk mai shirin sayen Ronaldo dai sai ya kawo sama da Dala Biliyan guda.

Shugaban Kulob din dai ya zargi yadda ‘Yan jarida wajen yada lamarin harajin babban ‘Dan wasan wanda yace kai ka dauka an kama ‘Dan wasan da laifi ne. Rahotanni daga Kasar Sifen na nuna cewa Tauraron Dan wasan na shirin tashi daga Madrid bayan an fusata sa.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Dubi gidan Evans mai garkuwa da mutane

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel