Masu kokarin cin zarafin mu saboda suna kan mulki, su jira zasu ga ikon allah – Inji Sule Lamido

Masu kokarin cin zarafin mu saboda suna kan mulki, su jira zasu ga ikon allah – Inji Sule Lamido

- Alhaji Sule Lamido ya karbi bakwancin kungiyoyin matasan jihar Jigawa a gidansa

- Tsohon gwamnan yayi wa matasan albisir cewa nan da shekaru 30 masu zuwa zune manya kuma zasu zama abun alfahari da tinkaho a kasar

- Lamido ya ce Allah ne ya karba mulki a wajen su yaba jam’iyyar APC , kuma shine zai sake karba mulkin ya basu

- Lamido ya ci gaba da cewar masu kokarin cin zarafin su saboda suna kan mulki, ya ce su jira kwanan zasu ga ikon Allah

Jawabin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido yayin shan ruwa a gidansa na bamaina da kungiyoyin Sule Lamido Social Media Forum, Jigawa State PDP Consultative Forum da sauran kungiyoyi.

Shekaru 30 nan gaba masu zuwa kune manya kuma Insha Allahu zaku zama abun alfahari da tinkaho a kasar nan, domin dai matasan Jigawa suna da dukkan halayen kwarai a cikin yan Najeriya, kuma sun tashi akan hadin kan kasa da son zaman lafiya an koya musu mulki da yadda ake hada kan Jama'a

Masu kokarin cin zarafin mutane saboda suna kan mulki, suna wulakanta ‘yan Jam'iyyar mu saboda mun sauka su kuma sun hau, to su jira kwanan zasu ga ikon Allah.

Masu kokarin cin zarafin mu saboda suna kan mulki, su jira zasu ga ikon allah – Inji Sule Lamido

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido

Haka zalika Allah ne ya karba a wajen mu ya basu, kuma shine zai karba a wajen su ya bamu da iznin Allah.

Kamar yadda NAIJ.com ta samu daga shafin Rariya, jagoran wadda ya sake kira ga matasan jam'iyyar PDP a duk inda suke da su zama masu bin doka da oda, yace na koya muku tarbiyya da da'a da mutuntaka, na koya muku furuci da girmama na gaba da ku, amma ban koya muku tsoro ba ban yarda ku ji tsoron kowa ba akan gaskiya a kasar nan.

Muna kan bakar mu na kalmar da Buhari yayi amfani da ita cewar a kasa, a tsare, a jira kuma duk girman mutun kar ku bari yayi muku magudi ko waye shi.

KU KARANTA: Sanata Musiliu Obanikoro ya canza shake zuwa APC

Jam'iyyar PDP aikin ta shine abun yakin neman zaben ta, kuma Insha Allahu ko yanzu akai zabe zamu lashe.

Jagoran ya yaba da irin halin wakilci na kwarai da matasan suke nunawa kuma ya ce yana kallon duk abunda ake a kafafen soshiya midiya, ba shakka gobe tana da kyau, kuma Insha Allahu zaku ga nasarori a rayuwar mun yi muku addua kuma zamu cigaba da yi muku

A karshe ya yi adduar fatan alheri da addu'ar Allah ya mayar da kowa gidan lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda wani jami'in jam'iyyar APC mai mulki ya ce jam'iyyar na iya fadi a zabe mai zuwa 2019

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC

Makamai miliyan 350 marasa rajista Ke yawo a Najeriya - Kungiyar UNREC
NAIJ.com
Mailfire view pixel