Shin gaskiya ne an sace Dabinon Makkah a Najeriya? Kalli hotunan nan kafin ka yanke hukunci

Shin gaskiya ne an sace Dabinon Makkah a Najeriya? Kalli hotunan nan kafin ka yanke hukunci

- Dabinon Makkah da yayi layar zana ya dawo

- An rarraba ma yan gudun hijira dabinon da saudiya ta aiko

Wasu hotuna da suka bayyana a shafin jaridar Rariya sun bayyana yadda aka rarraba dabinon da ake ta takaddama akansu, wadanda kasar Saudiya ta aiko ma Najeriya.

Idan za’a iya tunawa, NAIJ.com ta ruwaito a baya cewa ofishin jakadancin kasar Saudiya dake Najeriya sun yi korafin an karkatar da dabinon da gwamnatin kasar ta Saudiya ta aiko ma gwamantin Najeriya domin raba ma gajiyayyu da yan gudun hijira.

KU KARANTA: Dan ƙasa na gari abin koyi: Idan ka ji abinda Dangote yayi, zai burge ka

Amma wadannan hotunan sun nuna da alamun wancan labara bai tabbata ba musamman yadda gwamnatin tarayya bata bada wani bayani gamsashshe ba dangane da zarge zargen.

Shin gaskiya ne an sace Dabinon Makkah a Najeriya? Kalli hotunan nan kafin ka yanke hukunci

Yayin rabon dabinon

A wani labara kuma, hukumar kula da yan gudun hijira ta musanta zargin satar dabinon, inda tace ofishin jakadancin ne da kansa ta raba dabinon ga kungiyoyi masu zaman kansu don rarraba ma yan gudun hijira.

Shin gaskiya ne an sace Dabinon Makkah a Najeriya? Kalli hotunan nan kafin ka yanke hukunci

Rabon dabinon

Sai dai jami’in kula da jama’a na hukumar yace basu da ikon hana yan gudun hijira siyar da dabinon, kamar yadda suka saba siyar da sauran kayayyakin tallafi da akan basu lokaci zuwa lokaci.

Ga sauran nan:

Shin gaskiya ne an sace Dabinon Makkah a Najeriya? Kalli hotunan nan kafin ka yanke hukunci

Rabon dabinon

Shin gaskiya ne an sace Dabinon Makkah a Najeriya? Kalli hotunan nan kafin ka yanke hukunci

Rabon dabinon

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Da gaske Najeriya giwar Afirka ne?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel