Hukumar yan sanda ta cafke gungun matasa yan fashin da dan shekara 22 ke jagoranta (Hotuna)

Hukumar yan sanda ta damke wasu ja’iran yan fashin da suke addaban Bodan Badagry da Seme a jihar Legas.

Yan fashin karkashin jagorancin wani dan shekara 22 sun shiga hannu ne bayan sun kaiwa wasu jami’an Kastam hari inda suka kwace mota kirar 2006 Toyota Corolla da Lexus 350 SUV.

Bisa ga umurnin Sifeto janar, rundunar jarimi Abba Kyari suka kai musu simame kuma sukayi ram da su.

Kyari a wata jawabin da ya saki, yace bayan kama yan fashi sun bayyana cewa sun kasance suna fashi da makami a wata Febrairu.

Hukumar yan sanda ta cafke gungun matasa yan fashin da dan shekara 22 ke jagoranta (Hotuna)

Hukumar yan sanda ta cafke gungun matasa yan fashin da dan shekara 22 ke jagoranta (Hotuna)

Daga cikinsu shine Tunji Adesanya, wanda aka saki daga kurkukun Agodi ba da dadewa ba tare da Rasaq Lawal wanda shine shugabansu.

Sauran sune Hammed Lawal, Olanrewaju Wasiu, Kenneth Ohmai, da Ibrahim Aliu dan jihar Edo.

Yace : “Yan fashin sun bayyana cewa lallai sun kai hari ga Mr. Garba Babayaro da Akubo Idris kuma tun ba yau ba suna fashi da makami a Badagry da Seme.

KU KARANTA: Wani azzalumi ya bugawa yaro kusa a kai

An kwace bindiga AK47 1, karamin bindigan gargajiya 1, carbin harsashi 84 da sauran su."

Yace ana cigaba da kokarin damke wadanda suka arce daga cikinsu.

Hukumar yan sanda ta cafke gungun matasa yan fashin da dan shekara 22 ke jagoranta (Hotuna)

Hukumar yan sanda ta cafke gungun matasa yan fashin da dan shekara 22 ke jagoranta (Hotuna)

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

NAIJ.com
Mailfire view pixel