N-Power: Mutane 753,307 suka yi rijista a shirin da ke bukatar mutane 300,000

N-Power: Mutane 753,307 suka yi rijista a shirin da ke bukatar mutane 300,000

- A cikin kwanaki 5 kacal da fara yin rajistar shirin samar da ayyukan yi na N-Power, mutane 753,307 ne suka yi rajista.

- Wannan adadi dai ya ninka na mutanen da suka yi rajista a shekarar 2016.

Mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman akan harkokin samar da ayyukan yi, Afolabi Imoukhuede shi ya bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN a jiya Lahadi a Asaba, babban birnin jahar Delta.

NAIJ.com ta samu labarin cewa ya ce a cikin kwanaki 5 kacal, an ninka adadin da aka samu a 2016, duk da cewa an shafe watanni 2 da rabi ana yin rajista a wancan lokacin.

Imokhuedu ya bayyana cewa bangaren koyarwa na shirin shi ya fi kawo mutane da rajistoci 470,456, yayin da shirin noma ya samu 127,315.

N-Power: Mutane 753,307 suka yi rijista a shirin da ke bukatar mutane 300,000

N-Power: Mutane 753,307 suka yi rijista a shirin da ke bukatar mutane 300,000

Bangaren kiwon lafiya ya kawo mutane 85,691, yayin da a sabon bangaren karbar haraji aka samu mutane 69,842.

A cewar mai bada shawarar, shirin ya samu wannan nasara ne saboda mutane yanzu sun gasgata shirin, sabanin a shekarar da ta gabata.

Sai dai ya ce duk da yawan mutanen da aka samu, gwamnati ba za ta iya daukar fiye da dubu 300 ba, gudun kar a kere kasafin kudin da aka warewa shirin a wannan lokaci.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani
NAIJ.com
Mailfire view pixel