A yi taka tsan-tsan gurin bin wannan hanya don guje ma afkuwar hatsari

A yi taka tsan-tsan gurin bin wannan hanya don guje ma afkuwar hatsari

Bishiyoyi sun fadi a hanyar da ya sada Mokwa zuwa Makerasakamakon ruwan sama mai karfi.

Wasu bishiyoyi sun fadi kafin a isa Mokwa a hanyar Mokwa-Makera sakamakon ruwan sama da aka kwana ana zubawa kamar da bakin kwarya, don haka ya kamata masu tuki su sani a lokacin da suke kama hanyar da ya lankwasa daga Bida zuwa Mokwa.

Ga hotunan yadda bishiyoyin suka fadi a kan hanya a kasa:

A yi taka tsantsan gurin bin wannan hanya don guje ma afkuwar hatsari

Hanyar da bishiya ya fadi

A yi taka tsantsan gurin bin wannan hanya don guje ma afkuwar hatsari

Bishiyan ya fadi ne a tsakanin hanyar Mokwa zuwa Makera

KU KARANTA KUMA: Abin al’ajabi: Wani masallaci da mata da maza ke ibada a tare

A wani al’amari makamancin haka, NAIJ.com ta kawo cewa hukumar sufurin jiragen kasa na Najeriya (NRC) ta ce za a dauki tsawon sati biyu a gyaran babbar gadar da ta hade garin Mokwa da Jebba sakamakon ruwan sama da ya lalata gadar jirgin kasan da ta mota a babbar hanyar da ta hada yankin arewacin Najeriya da kudanci a jihar Niger.

Yakubu Mahmud, wanda shine jami’in hulda da jama’a na hukumar ya bayyana cewa ruwan sama mai karfi da aka yi ya karya gadar titin jirgin kasa da hanyar mota tsakanin Mokwa zuwa Jebba kuma karyewar gadar ya haifar da kalubale wajen sufurin jiragen kasa daga Lagas zuwa Kano da kuma motocin da ke jigila daga kudu zuwa arewacin Najeriya.

Motocin da suka fito daga Lagas a yanzu haka dai ba su iya wuce garin Jebba cikin jihar Kwara, yayin da wadanda suka fito daga yankin arewaci ba su iya wuce garin Mokwa a jihar Niger.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal

Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal
NAIJ.com
Mailfire view pixel