Gwamnatin tarayya za ta daukaka kara akan wankewar da akayi wa Saraki

Gwamnatin tarayya za ta daukaka kara akan wankewar da akayi wa Saraki

- Gwamnatin tarayya ta ce wanke shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da kotu ta yi zai haifar da sakamako mara kyau a yakin da take da cin hanci da rashawa.

- A don haka ne ta yanke hukuncin daukaka karar, kamar yadda mai baiwa shugaban kasa shawara akan kararraki Okoi Obono-Obla ya fadawa manema labarai a Jiya Lahadi.

A makon daya gabata ne dai kotu ta wanke Saraki daga laifuka 18 da ake tuhumar shi da su da suka jibanci kin bayyana gaskiyar adadin kadarorin da ya mallaka.

NAIJ.com ta samu labarin cewa shugaban kotun, Danladi Umar ya bayyana cewa bangaren masu kara sun kasa gabatar da shedu kwarara akan Saraki.

Gwamnatin tarayya za ta daukaka kara akan wankewar da akayi wa Saraki

Gwamnatin tarayya za ta daukaka kara akan wankewar da akayi wa Saraki

Obono-Obla ya kira wannan hukunci abun al’ajabi. Ya ce nan da ranar Laraba mai zuwa gwamnatin za ta daukaka karar.

Shari’ar Saraki dai ta fara ne tun a shekarar 2015, inda ya yi duk iya kokarinsa, har izuwa kotun kololuwa domin ganin bai fuskanci shari’a ba, lamarin da yaki yiwuwa.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel