Dole kowa ya saka ragar sauro a cikin sadakin auren sa a jihar Sokoto

Dole kowa ya saka ragar sauro a cikin sadakin auren sa a jihar Sokoto

- Wani kudiri da ke neman zama doka a jihar Sokoto shi ne na batun sanya ragar sauro mai dauke da feshin maganin kashe sauro a kayan lefe da miji kan kaiwa mace bisa al’adar auren malam Bahaushe.

- Kunshin wannan doka na dauke da batun lalle namijin da ke neman auren mace ya sanya ragar sauro mai dauke da maganin kashe sauro ko kuma babu batun wannan aure a gwamnatance.

Daily Trust ta rawaito cewa kunshin dokar har lau na cewa “Dole ne ma’auratan su yi wani gwaji na sanin irin kwayar halittar da jininsu ke dauke da don kaucewa haihuwar ‘ya’ya masu cutar sikila”.

Kuma ma’auratan za su shiga tsarin gwamnati na adashin lafiya don saukakawa kansu kudin magani da kiwon lafiya a lokacin da bukatar hakan ta taso.

NAIJ.com ta samu labarin cewa Kwamishinan lafiyar jihar, Balarabe Kakale ya ce wannan doka in an tabbatar da ita za ta magance matsalolin lafiya da jihar ke fama da su.

Dole kowa ya saka ragar sauro a cikin sadakin auren sa a jihar Sokoto

Dole kowa ya saka ragar sauro a cikin sadakin auren sa a jihar Sokoto

Kakle ya ci gaba da cewa da zarar dokar ta fara aiki, dole masu shirin aure su yi gwajin cutar Kanjamau da na radadin hanta da a turance ake kira da Hepatitis B kafin a basu damar auren juna.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Sokoto ce ta dauki nauyin wannan doka kuma tuni ta mika dokar ga majalisar jihar

Za a gabatar da wani taron tattaunawa don tabbatar da matsayar addinin musulunci da al’ada akan shirin kafin a je ga aiwatar da dokar.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa

Buhari ya amince a sayo jiragen ruwa don toshe kafofin barna da samar da tsaro a hanyoyin ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel